21 Yuni 2020 - 08:14
​MDD Ta Bukaci A Kwantar Da Hankula A Kasar Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwantar da hankula a Mali bayan zanga-zangar ranar Juma’a da dubban al’ummar kasar suka gudanar kan neman shugaba Boubacar Keita ya yi murabus.

(ABNA24.com) Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwantar da hankula a Mali bayan zanga-zangar ranar Juma’a da dubban al’ummar kasar suka gudanar kan neman shugaba Boubacar Keita ya yi murabus.

Babban magatakardar Majalisar Antonio Gutteres ta bakin mataimakinsa Farhan Haq ya nemi bangarorin adawa su daina tunzura magoya bayansu, domin kada hakan ya yi sanadiyyar sake rikicewar kasar da ke fama da hare-haren ta’addanci tun shekaru 8 da suka gabata.

Zanga-zangar ta ranar Juma’a ita ce irinta ta biyu a watan nan, inda bangaren adawa ya sha alwashin bijire wa umarnin gwamnati, tare da nemen shugaba Keita ya sauka daga kan mulki.

Boubacar Keita wanda aka sake zabensa a 2018, tun bayan sake hawansa a kan kujerar mulki lamurran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar ta Mali, baya ga rikicin siyasar kasar kuma, akwai karuwar rashin aikin yi da kuma yawaitar yajin aikin ma’aikata galibi malaman makaranta.

Shugaba Keita dai ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tattaunawa kai tsaye tare da bangarorin da suke yin bore domin a salubo hanyoyin warware matsalolin da kasar take ciki.


/129